Saturday 14 September 2013

KACICI KACICI

1-  Salamun gaisuwa tagari,
2-  Ga Manzo na abin fahari,
3-  Sahabbai masu yin witiri,
4-  Da alaye da ke da gari!
5-  Tabaraka mai dukkan lamari,
6-  Ka ɗauke min duhun kabari,
7-  Gare ka na ke daɗin zikiri,
8-  Ka ban ’yar nan abar garari!
9-  A yau dai na fito sarari,

10-  A yaƙin ban ganin haɗari,
11-  Kamar yaro a ba shi ɗari:
12-  A murna ya fi mai digiri!
13-  Abokai na ku yo nazari:
14-  Ga rana ta fito sarari,
15-  Ta na haske, ta na ta fari,
16-  Hasken rai na abar marari!
17-  Budurwa ce fara tagari,
18-  Mai murya sai ka ce kanari,
19-  A baitoci da ke waɗari,
20- A ƙauye ko cikin sa gari!
21-  Da ke ce yau na ke fahari,
22-  A zuci a yau ina tiriri,
23-  Soyayya ta saka ni jiri,
24-  Batun ƙaunar ki ba ni bari!
25-  Mai so na sai mu ƙara shiri,
26-  Mu sha zaƙi na so nagari,
27-  Shi zaƙin sai ka ce sikari,
28-  Tsaya kai na ki na jimiri!
29-  Abar ƙauna abar garari,
30-  Kin taka rawa kamar mazari,
31-  Me zan ce ne ki ba ni gari,
32-  Har in dace da ke tagari?
33-  Mafarki na abar marari,
34-  In rintse ido kamar kanari,
35-  In farka ga ki nan sarari
36-  A tare da ni mu na bidiri!
37-  In buɗe ido cikin katari,
38-  A ce ni ne na cinye gari,
39-  A ɗaki na ki ke witiri,
40-  A lallai da’iman lamari!
41-  Kira na sai mu ƙara shiri,
42-  Ga Allah mui ta yin witiri,
43-  Nabiyyul Lahu nai zikiri,

44-  Ku ce amin da ayyiriri!


-----------Godiya ta musamman ga: Ibrahim shema Da Bashir muhammad idris

1 comment:

  1. 45- Kwarai wakarka tai tsari
    46- Akan so ka zamo mazari
    47- Ka tsaro baitika na gari
    48- Allahu yasa mu sha budiri
    49- Da ɗo himma ka kara shiri
    50- Dan so shi zai cireka mari
    51- Musamman inda alkawari
    52- Mai doki bai hawa kutiri
    53- Mu roki tabara duk buri
    54- Mu guje surkulle ko bori
    55- Idan burinmu yafi dari
    56- Mu Allah bashi yin gori
    57- Inama dai ka sa gishiri?
    58- Cikin baitinka kai kari
    59- Kamanninta ka bamu labari
    60- Kicibis! ko zamu ganta agari
    61- Muyo mata addu’ar khairi
    62- Domin Allah ya bata tsari
    63- Cikin zuciya ta baka guri
    64- Ko ka wuce mai nufin sharri
    65- Anan zan dakata bashari
    66- Ina murane da dan tari
    67- Yasa zancen danai kudiri
    68- Tilas ya takaita sai hakuri.

    ReplyDelete