Monday 14 October 2013

05 Cigaban HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN

                                        ***Wannan goron sallah ne readers***

Al'adar garin ce idan mutum ya mutu,'ya 'yansa ne za su gaji dukan dukiyarsa,idan kuwa ba shi da 'ya 'ya, to 'yan uwansa ne za su gaje shi, idan babu kuma sai matarsa ta gaje shi, 
idan ba shi da mata sai a saka dukiyarsa a baitulmali.

Bayan mutuwar Kasim,kasancewar ba shi da 'ya 'ya, sai Ali Baba ya gaji dukan dukiyarsa, da gidansa da kuma kuyangar nan tasa mai tsananin hikima, watau Murjanatu.
Ali Baba ya kwashe dukan dukiyar da ya samu daga taskar 'yan fashin nan ya koma gidan Kasim tare da matarsa. Ita kuma matar Kasim ta koma gidan mahaifinta.

A cikin wannan halin ne barawon nan ya hilaci dattijo Baba Mustafa har ya kawo shi gidan da Ali Baba ya ke ciki da matarsa da kuyangarsa.
Kuma ya yi wa gidan 'yar alama da bakin fenti yadda idan suka dawo cikin dare tare da sauran barayin za su yi saurin shaida gidan.

Bayan barawo ya koma wurin 'yan uwansa, cike da farin cikin gane gidan Ali Bab, ya shaida musu cewa bukata ta biya. Barayi suka yi murna da wannan labari.
Babban su ya ce, "Kowa ya zauna cikin shiri, domin yau cikin dare za mu tafi mu kashe wannan mutum, sannan mu kwashe dukan dukiyar da muka samu a cikin gidansa.
" Barayi duka suka shirya suna jiran dare ya yi.

Ashe kuma bayan tafiyar barawo da Baba Mustafa daga kofar gidan Ali Baba, Murjanatu ta fito domin ta kai sako wani gida.
Bayan ta dawo, har za ta shiga gida, sai ta kyalla ido ta ga an yi wata 'yar alama da bakin fenti a jikin kofar gidansu.
Ta duba kofar makwabtansu ba ta ga irin wannan alama ba. Ta kuma duba wani gidan, ba ta ga wannan alama ba, ta sa hannu wai ta goge alamar, amma ta ki goguwa.
Sai jikinta ya ba ta lalle wannan alama da aka zana a kofar gidansu akwai wata manufa a ciki, ruwa ba ya tsami banza.

Murjanatu ta shiga gida ta samo bakin fenti, ta bi dukkan kofofin gidajen makwabtansu ta yi musu irin 'yar alamar da ta gani a kofar gidansu.
Ta ja bakinta ta tsuke, ba ta fada wa kowa ba.

A cikin daji kuwa, barayi sun shirya tsab domin tunkarar gidan Ali Baba, Da lokaci ya yi, suka shirya suka nufo gari.
Da suka iso bakin gari, sai suka dakata sai da dare ya raba tsakiya, ba a jin motsin komai a cikin garin, sannan suka shiga.

Barawon da ya gane gidan yana gaba suna biye da shi har suka iso unguwar da gidan Ali Baba ya ke ciki.
Da zuwansu, sai suka shiga haska fitulu a kofar gidajen domin gano gidan da barawo ya yi wa lamba.
Can sai wani daga cikinsu ya ce, "Ga alamar nan a jikin kofar wancan gidan." Wani kuma ya ce, "A'a, ga gidan nan." Can sai kuma wani ya kyalla ido ya ga alamar a jikin kofar wani gidan dabam.

Da barayin nan suka duba da kyau, sai suka ga ashe duka gidajen unguwar an yi musu lamba.
Sai shugaban 'yan fashi ya dubi barawon da suka aiko ya ce, "Sai ka nuna mana gidan da ka gano."

Barawo cikin kaduwa ya ce, "Wallahi ni gida guda na yi wa lamba, ban san me ke faruwa ba."

Shugaban barayi ya ce, "Wane ne daga cikinsu ka yi wa lamba?"

Barawo ya duba, ya kara dubawa, ya kasa gane gidan da Baba Mustafa ya nuna masa. Sai ya ce, "Wallahi ba zan iya shaida shi ba a halin yanzu."

Shugaban barayi ya fusata ya ce, "Ka san ba za ka iya gane gidan ba ka sa muka zo, muka yi wahalar banza, za mu koma a banza a wofi? Lalle hukunci zai hau kanka.
" Ya ba da umurni aka daure wannan barawo a kan dokinsa, suka kora shi suka nufi cikin daji, wurin maboyarsu.

Da suka isa wurin da dutse ya ke, suka bude shi suka shiga daga ciki.
Shugaban 'yan fashi ya sa takobinsa ya dauke kan barawon nan da ya kasa gane gidan Ali Baba.
Sannan ya juyo ga sauran barayi ya ce,"Wa zai faranta mini rai, ya shiga cikin gari ya gano mana gidan mutumin nan, ni kuwa in saka masa da abinda duk ya ke bukata?"

Duk barayin nan suka yi jim, can sai wani ya yunkuro daga cikinsu ya ce, "Ni zan tafi, kuma ba zan dawo ba sai na gano takamaiman gidan wannan mutumin,
idan kuma ban gane ba na yarda a zartar da hukuncin kisa a kaina, kamar yadda aka yi wa na farko."

Barawo ya yi shiri, ya canja kamanninsa kamar wani mutumin kirki, ya nufi cikin gari. Da ya isa cikin gari, sai ya tasar wa rumfar Baba Mustafa, baduku.
Ya same shi zaune yana dinkin wata jakar fata.

Barawo ya yi amfani da dabarar da abokinsa na farko ya yi, ya ja hankalin dattijo da kudi, har ya kai shi dai dai kofar gidan Ali Baba.
Bayan da ya sallami dattijon, sai ya dauko jan fenti a cikin jakarsa, ya sami wani wuri a jikin gidan,
wanda ba duka idon mutum zai yi saurin kaiwa ga wurin ba, ya yi 'yar alama wadda za ta sa ya gane gidan.

Bayan ya tafi, sai Murjanatu ta fito zuwa wurin da aka aike ta. Bayan ta dawo, kafin ta shiga gida sai kuwa idonta ya kai ga alamar da barawon nan ya yi da jan fenti.
Ta tsaya tana tunanin shin wai me ake nufi da wadan nan alamomi da ake yi musu a jikin gida? Ta je ta samo kalar fentin,
ta bi dukan gidajen makwabtansu ta yi musu irin wannan 'yar alamar.
Ta shiga gida ba ta fada wa kowa ba.

Shi kuwa barawo da ya koma sai ya shaida wa shugabnsu cewa ya gane gidan,
don haka su shirya da dare su shiga gari su kashe mai gidan sannan su kwashe dukan dukiyar da suka samu a cikin gidan.

Da lokaci ya yi, barayi suka shirya suka shiga cikin garin da dare, lokacin kuwa duk mutane kowa ya yi barci, suka tasar wa unguwar da Ali Baba ya ke da iyalinsa.
Da isarsu sai shugabansu ya ce da barawon nan, "Maza nuna mana gidan mu aikata abin da ya kawo mu, mu juya kafin gari ya waye."

Barawo ya haska fitilarsa a jikin gida na farko, dai dai inda ya san ya yi alama, sai kuwa ga 'yar alamar da jan fenti.
Har za su balle gidan su shiga, sai shugabansu ya ce, "Bari mu fara tabbatar wa da kanmu cewa wannan shi ne gidan da muke nema, kada a sami kuskuren da aka samu jiya,
ku tafi ku haska sauran gidajen, idan babu wani gida mai irin wannan alama, to wannan shi ne gidan da muke nema."

Sauran barayi suka warwatsu cikin unguwar, duk gidan da suka haska fitilarsu sai su ga irin wannan alama a jiki.
Suka zo suka fada wa shugabansu. Shugaban ya tambayi barawon ko zai iya gane gidan a cikin sauran gidajen da suke da alama iri daya? Barawo ya ce ba zai iya ba.

Suka koma maboyarsu. Shi ma wannan barawo aka zartar masa da hukuncin kisa.
Da shugabansu ya ga cikin dan kankanin lokaci ya yi asarar mutum biyu daga cikin yaransa, sai ransa ya baci, ya yi fushi, fushi mai tsanani.
Ya yi rantsuwa da abin da zai kashe shi cewa, shi da kansa zai shiga gari ya gane ainihin wannan gida da suke nema, wanda ya yi sanadiyyar rasa yaransa biyu.
Lalle mai wannan gida zai dandana azaba mai tsanani kafin su kashe shi.

Washe gari shugaban barayi ya yi shiri da kansa ya shiga gari. Ya yi amfani da dabarar da barayin nan biyu suka yi amfani da ita, ta saye dattijo baduku, watau Baba Mustafa da kudi.

Da suka zo kofar gidan, shugaban barayi ya sallami dattijo. Ya dubi gidan da kyau tun daga kasa har bisa, ya yi murmushi ya ce a ransa, "Yaro dai yaro ne, i
n ba halin yarinta ba mene na abin yi wa wannan gida alama? Wannan makeken dutsen da ya ke kwance gab da kofar shiga gidan ai ya isa alamar da za a gane gidan,
ko ba shi ba ma, waccan tsagawar da bangon gidan ya yi ita ma alama ce babba ta gane gidan." Ya sake yin murmushi, ya dubi gidan ya ce,
"Mai gidan nan yau kwananka ya kare, Allah ya kai mu dare." Ya koma gun 'yan uwansa.

Da Murjanatu ta fito daga gida, bayan tafiyar shugaban barayi, ta tsaya ta duba jikin gidansu da kyau ko za ta ga wata sabuwar alama, amma ba ta gani ba.
Ta ce a ranta, "Wata kila mai yi musu lamba a jikin gida ya gaji ya watsar, ko wane ne? Oho! Wata kila ma yara ne." Ta kama harakokin gabanta, ba ta koma kan batun ba.

***BARKA DA SALLAH,ALLAH YA MAIMATA MUNA

Ga dukan alamu an kusa a kashe BOSS. Ku biyo mu don jin karshan labarin
Naku Waziri Aku
#Nishaaaddi_Management

Sunday 13 October 2013

04. HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN

Bayan kwana biyu,barayi suka koma maboyarsu, ga tsananin mamakinsu sai suka tarar da an dauke gawar mutumin da suka kashe, bayan wannan kuma an sake dibar musu dukiya.Cikin fushi, bakinsa na kumfa, babban yan fashin ya ce, "Ina rantsuwa da abin da zai kashe ni, hankali na ba zai kwanta ba har sai na nemo wanda ya gane sirrinmu, yana zuwa yana dibar mana dukiya, ko wane ne shi, kuma ko a ina ya ke cikin duniyar nan. Idan kuwa na same shi zan gana masa azabar da ba a taba yi wa wani abu mai rai irinta ba, kafin na kashe shi!" Ya ci gaba da cewa, "Ina so daya daga cikinku ya yi shiri irin na fatake, ya shiga cikin birni ya shako mana labari daga mutane, wata kila zai ji ana labarin wani mutum da aka kashe ta hanyar daddatsa jikinsa, ta haka za mu gane wanda ya zo nan ya dauke shi, kuma ya ke dibar mana dukiya." Sai wani barawo daga cikinsu ya ce, "Ni zan tafi, kuma na yi alkawrin ba zan komo nan ba sai da cikakken labarin wannan mutum." Babbansu ya ce, "Wannan aiki ne mai muhimmanci a wurinmu gaba daya, saboda haka idan har ka yi kuskuren da ka dawo nan ba tare da ka gano mana gidan wannan mutumin ba, to zan kashe ka." Barawo ya ce ya yarda. Ya yi shiri irin na matafiya, idan ka gan shi kamar wani mutumin kirki. Ya nufi birni. Ya iso cikin garin da sassafe. Da shigarsa cikin gari, sai ya hango wani mutum ya yi sammakon bude rumfarsa yana zaune a ciki. Da ya isa inda wannan mutumin ya ke, sai ya ga ashe dattijo ne, yana zaune yana dinkin takalmi. Ya yi mamakin wannan dattijo da yadda ya yi sammakon bude rumfarsa, bayan duk sauran rumfuna suna a rufe. Barawo ya yi wa dattijo sallama. Bayan ya zauna sun gama gaisawa sai ya ce masa, "Baba, amma Allah ya hore maka kaifin ido, ta yaya kake iya gani cikin duhun safiyar nan har kake dinki, ga shi kuma ka tsufa?" Dattijo ya ce, "Ga alama dai kai bako ne a wannan gari namu, idan ba haka ba waye bai sanni ba da kuma lakanin da ake yi mini na 'Baba Mustafa, dila mai idon zinari' ba. Tun ina dan shekara takwas na koyi wannan sana'a ta dinki daga mahaifina, kuma tun lokacin ita nake yi. Kai bari ma ka ji, saboda gwanancewata a dinki, har gawar mutum na taba hadawa na dinke ta wuri daya, bayan da barayi suka yi mata gunduwa-gunduwa, kuma a cikin daki mai duhu na yi wannan aiki." Barawo ya bude baki cikin mamaki, ya ce a ransa, ga dukkan alamu na taki sa'a a kan wannan bincike da na fito yi, lalle ta hanyar dattijon nan zan sami abin da na fito nema. Ya dubi Baba Mustafa cikin mamaki ya ce, "Ka taba dinke gawar mutum fa ka ce? Kuma a cikin daki mai duhu? Wannan basira taka da yawa ta ke. Amma dai tun kana dan saurayinka ka yi wannan aiki ko?" Baba Mustafa ya yi dariya ya ce, "Ba a yi kwana hudu da na yi wannan aiki ba. Wata rana ne, da sassafe kamar yanzu, wata yarinya.... Af! Na manta an rantsar da ni a kan cewa kada na yi wannan zance da kowa." Da jin haka, sai barawo ya jawo jakarsa, ya bude ta sosai ta yadda Baba Mustafa zai iya ganin kudin da ke ciki. Ya lura da yadda Baba Mustafa ya yi ajiyar zuciya lokacin da ya ga kudin da ke makare a cikin jakar. Ya debo kudin ya ba shi, ya ce masa, "Karbi wannan ka fitar da kono a kan rantsuwar da ka yi, ina so ka fada mini wannan labari, kuma ka kai ni gidan da ka yi wannan aiki. Idan ka yi mini wannan, hakika zan biya ka da kudi mai yawan gaske." Baba Mustafa ya ce, "Idan dai za ka biya ni ai sai na fada maka labarin duka." Barawo ya debo kudi mai yawa ya ba Baba Mustafa. Shi kuma ya fede masa biri har wutsiya. Barawo ya ce, "Tashi mu je maza ka kai ni gidan, kafin mutane su fara fitowa zuwa wurin harkokinsu." Baba Mustafa ya ce, "Ba ka ji labarin dai dai ba ne? Ai yarinyar rufe mini ido ta yi lokacin da za ta kai ni gidan, ba ta bude mini ido ba sai da muka shiga cikin dakin da gawar ta ke. Kuma ina gama aikin ta sake rufe mini ido, sai da muka zo nan sannan ta bude. Ba zan iya gane gidan ba, ko kalar fentinsa ban samu damar gani ba ballantana na ce zan iya shaida shi." Barawo ya ce, "Ka yi amfani da hikimarka da basirarka mana, ni ma in rufe maka ido ka rika misalta hanyar da kuka bi a cikin zuciyarka har mu isa gidan. Ina tsammanin za ka iya yin wannan." Baba Mustafa ya ce, "Kwarai kuwa zan iya, domin duk kwanar da muka bi zan iya kiyasta ta a cikin zuciyata. Kai bari ma ta wannan, har takun da muka yi kafin mu isa gidan da kuma bayan mun dawo na lissafe su kaf. Ba fa banza ake yi mini lakabi da dila ba yaro." Suka tashi, barawo ya sami wani kyalle ya rufe idon Baba Mustafa. Suka shiga cikin gari. Bayan sun dan taba tafiya ta wani lokaci, sai suka iso gaban wani gida. Baba Mustafa ya tsaya, ya ce da barawon nan, "A dai dai nan ne na ji yarinyar nan ta bude kofar gida muka shiga daga ciki." Barawo ya bude wa Baba Mustafa fuskarsa, ya ce, "Ka tabbata wannan gidan ne?" Baba Mustafa ya tabbatar masa da cewa ko shakka babu. Barawo ya dubi gidan nan da kyau, da kalar fentinsa. Ga mamakinsa sai ya ga ai kusan duka gidajen unguwar kalar gininsu guda, kuma duk fentinsu kala guda ne. Sai lamarin ya daure masa kai, ya ga cewa idan ya koma ya fada wa 'yan uwansa ya gane gidan, idan suka zo cikin dare ba zai iya shaida gidan har ya nuna shi ba. Don haka sai ya bude jakarsa ya dauko wani bakin fenti da yayi amfani da shi wajen canja kamannunsa, ya zana wata 'yar alama a jikin kofar gidan, yadda idan suka dawo cikin dare zai gane gidan. Ya sallami Baba Mustafa ya koma rumfarsa. Shi kuma ya juya zuwa cikin daji wurin 'yan uwansa domin ya shaida musu cewa bukata ta biya. *** ZA MU CI GABA INSHA'ALLAHU#NishaaaddiWaziri Aku: 

Wednesday 9 October 2013

03. HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN


***Ci Gaban Labari****
 Kofa na budewa,sai Kasim ya fito waje da gudu,ya bangaje wasu daga cikin barayin nan. Kafin ya sake daga kafarsa wani daga cikin barayin nan ya raba shi gida biyu da takobinsa,gaya-wa-jini-na-wuce.

 Barayin nan suka shiga cikin dutsen,suka ga mangalolin da Kasim ya cika da dukiyarsu.
 Kuma suka lura da cewa lalle ko bayan wannan dukiyar da Kasim ya dauka,akwai alamun an taba dibar dukiyar,ke nan ko Kasim din ne ya taba diba yanzu ya dawo ya kara, ko kuwa akwai wani bayan Kasim din wanda ya dibar musu dukiya. 

Suka yi mamakin yadda Kasim ya san kalmomin da ake fada dutsen ya bude. 
Domin su gargadi duk wani mai zuwa yana dibar musu dukiya,sai suka raba gangar jikin Kasim gida hudu, suka manna kowanne sashe daya a bango daya na dutsen,watau kudu da arewa,gabas da yamma.

Suka fita suka kora jakunansa zuwa inda suke tara dabbobin da suke satowa.
Da dare ya yi matar Kasim ba ta ga ya komo gida ba,sai hankalinta ya fara tashi.

Ta dauki mayafinta ta ruga da gudu zuwa gidan Ali Baba.Ta same shi yana zaune yana hutawa.
Bayan sun gaisa, sai ta ce masa,"Ya kai dan uwan mijina,na san cewa kana da labarin mijina ya shiga daji da jakai, tunda assalatu,akan zai samo wani abu a can,wanda bai fada mini ko mene ne ba.

Ga shi har dare ya yi bai komo ba. Shi ne na zo gare ka na ji ko ka san wurin da ya tafi? Ina jin tsoro ko wani mummunan abu ya faru da shi" Ali Baba ya ce da ita, "Haka ne, dan uwana ya fada mini zai shiga daji, ai na dauka ya dawo,amma bari yanzu na shirya na tafi neman labarinsa. 

Ki koma gida zan sanar da ke abin da ake ciki idan na dawo." Ali Baba ya tashi cikin daren nan ya daura wa jakansa uku mangaloli, ya kora su ya nufi cikin dajin da dutsen 'yan fashin nan ya ke. Can zuwa tsakiyar dare ya isa inda dutsen sihirin ya ke. Da isarsa gindin dutsen ya haska fitilarsa, sai ya ga jini faca-faca ko'ina a gindin dutsen. Tun daga nan sai ya sha jinin jikinsa. 

Ya ce,"Fayau bude dutsen simsim." Nan take kofa ta bude,ya shiga ciki. Da shigarsa sai kofa ta rufe,ya haska fitilarsa,sai ya ga gawar dan uwansa Kasim,an datsa ta gida hudu,an manna kowane datse a bangon dutsen. 

Nan take ya yi sauri ya harhada su wuri daya. Sannan ya kuma dibar dukiyar da jakansa biyu za su iya dauka, ya fita daga cikin dutsen. Ya dora wa jakinsa daya gawar dan uwansa, sauran biyun kuma ya dora musu dukiyar da ya diba,ya samu kiraren itatuwa ya rurrufe mangalolin da su,yadda mutane ba za su gane abin da aka dauko ba. 

Ya kora su da sauri ya nufi gida. Can zuwa da hantsi Ali Baba ya isa gida,ya shiga da jakansa biyu masu dauke da dukiyar cikin gida,ya fada wa matarsa ta sauke kayan ta boye su inda suka boye na farko. Ya kora jakin daya zuwa gidan matar dan uwansa.

 Da ya isa gidan sai ya kwankwasa kofa. Bayan kwankwasawa ta biyu, sai ya ga Murjanatu ta bude kofar. Murjanatu ta kasance baiwa ce ga Kasim, Allah ya hore ma ta tsananin wayo da dabara, duk da ta kasance yarinya karama, mai kananan shekaru, amma hankalinta da tunaninta ya zarta na manyan mutane. Shi ya sa ma duk wata shawara da ita Kasim ya ke yi.

 Ali Baba ya kora jakinsa cikin gidan, Murjanatu ta mayar da kofa ta rufe, ya umurce ta da ta kira masa matar dan uwansa. Bayan sun koma, ya sauke gawar Kasim ya shaida musu abin da ya faru da Kasim duka.

 Bayan sun gama yan koke-kokensu, sun share hawaye, sai ya ce musu, "Abin da na ke so da ku shi ne, ina so mutanen garin nan su tabbatar da cewa dan uwana ya mutu ne a gida, a kan gadonsa, sanadiyyar rashin lafiya, ba na so kowa ya san abin da ya faru da shi." Abin da ya sa Ali Baba ya fadi haka kuwa shi ne, ya tabbata idan barayin nan suka koma maboyarsu ba su ga gawar Kasim ba, za su shiga binciken wanda ya zo ya dauke ta. 

To idan mutanen gari suka san gaskiyar labarin yadda Kasim ya mutu, da yadda aka rufe gawarsa guntu-guntu, labarin ba zai boyu ga barayin nan ba, kuma za su yi saurin gane Ali Baba su kashe shi. 

Amma idan mutanen gari suka san cewa Kasim ya mutu ne a kan gadonsa sanadiyyar rashin lafiya, kuma an yi jana'izarsa gaban mutane, shi ke nan babu wanda zai koma ta kan batun. Don haka babu yadda za a yi barayin su gane wanda ya dauke gawar. Bayan Ali Baba ya tafi, sai matar Kasim ta ce da Murjanatu, "Na bar wannan a hannunki, ke kika san dabarar da za ki yi, ki kawar da hankalin mutane har su dauka cewa Kasim ya mutu ne sanadiyyar rashin lafiya a kan gadonsa." Murjanatu ta ce, "Wannan abu ne mai sauki a wurina." Sai ta ruga da gudu zuwa shagon wani mai sayar da magunguna, hankalinta a tashe, ko takalmi babu a kafarta, ta ce da shi, "Don Allah yi sauri ka bani maganin zazzabi, ubangijina Kasim na can zazzabi mai zafi ya rufe shi, har ba ya iya gane masu zuwa wurinsa." Mai magani ya dauko wani magni ya ba ta.

 Ta karba ta ba shi dirhami daya, ba ta ko tsaya karbar canji ba, ta nufi gida da sauri, ta na rike da magani a hannunta, tana tafe hawaye na fita daga idonta. Duk wanda ta hadu da shi a kan hanya, idan ya ga halin da take ciki, ga kuma magani a hannunta, sai ya tausaya mata, ya kuma gane abin da take ciki na jiyyar mara lafiya. 

Ali Baba da matarsa suka dinga Safa da Marwa tsakanin gidansu da gidan Kasim, domin dai su baddalar da mutane a kan cewa wani abu na faruwa a gidan Kasim. Don haka lokacin da mutane suka ji kuka daga gidan Kasim tare kuma da labarin mutuwarsa cikin dare ba su yi mamakin hakan ba. 

Tun da sassafe kafin Ali Baba ya gama shaida wa mutane labarin mutuwar dan uwansa Kasim, domin yi masa jana'iza, ita kuwa Murjanatu sai ta nufi shagon wani baduku, dattijo mai suna Baba Mustafa, domin dama dabi'arsa ce da an fito daga sallar subahi yake bude shagonsa. 

Ta same shi a zaune cikin shagon, bayan ta yi masa sallama sun gaisa, sai ta ce da shi, "Baba Mustafa ina da wani aiki da nake so ka yi mini yanzu, amma da sharadi daya." Ta dauko dinari daya ta danka masa a hannu. 

Ya yi sauri ya karbe yana murmushi, dama idonsa idon kudi kamar wuta da auduga ne, ya ce da ita, "Diyata, fadi abin da kike so na yi miki, ko menene idan dai zan iya yin sa, to zan yi miki shi duk da dai ban san ki ba, ban ma taba ganin ki ba." Murjanatu ta ce da shi, "Jiya cikin dare barayi suka shiga gidanmu suka kashe mijina kuma suka sassara shi guntu-guntu. 

Ina so, a matsayinka na baduku, ka harhada gawarsa wuri daya ka dinke, yadda za a ji dadin yi masa jana'iza. Amma da sharadin zan rufe fuskarka da mayafi ta yadda ba za ka iya gane hanyar da muka bi zuwa gidan ba, kuma ba za ka iya gane gidan ba. Haka kuma idan ka gama zan sake rufe fuskarka na maido ka shagonka. Zan biya ka kudi mai yawa, ka yarda da wannan sharadi?" Baba Mustafa ya ce ya amince.

 Murjanatu ta rufe masa fuska, ta ja hannunsa har suka isa gidan, ta bude kofa suka shiga ciki, ta ja shi har cikin dakin da gawar Kasim ta ke, sannan ta bude masa ido. Ta ce ya yi sauri ya hada shi masu jana'iza na nan zuwa. Nan take kuwa ba tare da bata lokaci ba Baba Mustafa ya dinke gawar Kasim wuri daya, kamar ba a taba sassara ta ba. 

Murjanatu ta ba shi kudi masu yawa, sannan ta rufe masa idanu ta mayar da shi shagonsa. Aka yi jana'izar Kasim aka gama ba tare da kowa ya san gaskiyar abin da ya faru gare shi ba. Su kuma barayin nan bayan kwana biyu suka koma maboyarsu, ga tsananin mamakinsu sai suka tarar da an dauke gawar mutumin da suka kashe, bayan wannan kuma an sake dibar musu dukiya. 

Cikin fushi, bakinsa na kumfa, babban yan fashin ya ce, "Ina rantsuwa da abin da zai kashe ni, hankali na ba zai kwanta ba har sai na nemo wanda ya gane sirrinmu, yana zuwa yana dibar mana dukiya, ko wane ne shi, kuma ko a ina ya ke cikin duniyar nan. Idan kuwa na same shi zan gana masa azabar da ba a taba yi wa wani abu mai rai irinta ba, kafin na kashe shi!" 

*** *** *** ZA MU CI GABA DA IKON ALLAH. *** *** ***
                                 -----____kuyi hakuri damu____-----

Saturday 28 September 2013

02 HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN


Lokacin da Kasim ya dawo daga kasuwa tun bai huta ba,matarsa ta tare shi ta ce,
"Maigida,na san da cewa ka dauki kanka a matsayin wanda ya fi kowa arziki a duk fadin garin nan,
to amma abin da ba ka sani ba shi ne,yanzu akwai wanda ya dame ka ya shanye game da arziki cikin wannan gari namu. 
Domin yana da tarin zinariyar da ta fi karfin a kidaya ta da hannu sai dai a auna ta da mudu."

Kasim ya ce,"Wane ne wannan attajiri haka,amma dai bai dade da zuwa garin nan ba ko?"
Matar ta ce,"Ba kowa ba ne face dan uwanka Ali Baba." Ta kwashe dukkan labarin yadda matar Ali Baba ta zo aron mudu a wurinta,
da kuma dabarar da ta yi har ta gano abin da aka auna da mudun. 

Kasim ya kasance ba ya kula da taimakon dan uwansa Ali Baba duk da tarin dukiyarsa,
ba ya ko yarda ya matso kusa gare shi,wai kada ya shafa masa talauci.
Da ya ji wannan labari daga matarsa,sai ya cika da mamaki tare kuma da hassadar jin cewa wai har akwai wanda ya fi shi arziki a garinsu. 
Ya ce a cikin ransa,"Yanzu dare ya yi,amma gobe tunda safe zan je gidan dan uwana na ji inda ya sami wannan dukiya da rana tsaka.Lalle idan ya fara sata ne,
zan tsegunta wa Sarki a daure shi." Ya kwanta amma ya kasa yin barci,yana ta kahon dandi har gari ya waye.

Da gari ya waye,tunda sassafe Kasim ya sallama wa Ali Baba.Bayan ya fito,ko gaisawa ba su yi ba,sai Kasim ya ce,"Ali Baba ka yi wa mutane badda sau,
suna ganin ka a matsayin talaka wanda bai mallaki komai ba sai jakai guda uku da kake zuwa daji kana yiwo itacen siyarwa.
Amma abin mamaki, jiya bayan na dawo daga shagona,matata ta ba ni wannan kwayar zinariyar ta ce mini a cikin mudun da ta ara muku ta makale.
Wannan ya tabbatar mata da cewa ba hatsi kuka auna da mudun ba.
Wannan ne dalilin da ya sa yanzu na yo maka sammako domin na ji inda ka sami wannan dukiya, 
idan kuwa ka ki fada mini zan je na shaida wa Sarki cewa kana daya daga cikin barayin nan da suka addabi mutanen wannan gari da kewayensa da sata,
yanzu haka ma zinariya na nan kime a gidanka da kuka sato. Kuma na tabbata idan aka bincike gidanka kaf,za a gan ta."

Da Ali Baba ya ji wannan zance na dan uwansa,sai ya tabbatar da cewa matarsa ta fallasa musu sirrinsu ba tare da ta sani ba,
don haka babu wani boye-boye illa ya fada wa dan uwansa gaskiyar abin da ya faru.

Ali Baba ya kwashe labrin abinda ya faru duka ya fada wa Kasim.
Ya yi masa kwatancen dajin nan da kuma dai dai wurin da dutsen da barayin nan suke tara dukiyarsu ya ke. 
Ya kuma fada masa abin da ake cewa dutsen ya bude da kuma abin da ake cewa ya rufe.

Kasim na gama jin wannan labari,bai zame ko'ina ba sai kasuwa.Ya siyo jakai guda goma,kowane da mangalarsa,ya kawo gida ya daure.
Tun da asuba ya daura wa jakuna mangaloli, ya nufi dajin nan da Ali Baba ya yi masa kwatance. Can zuwa rana tsaka ya isa,
ya bi kwatancen da aka yi masa har ya gano wurin da dutsen ya ke. Ya daure dabbobinsa a kusa da dutsen.

Ya tsaya gindin dutse ya ce,"Fayau, bude dutsen Simsim." Rufe bakinsa ke da wuya, sai ya ga kofa ta bude daga jikin dutsen. Mamaki ya rufe shi, 
nan da nan ya kwanto mangaloli daga jakunansa ya kutsa kai cikin dutsen, yana shiga dutsen ya rufe.

Kasim ya ga ashe dutsen wani katon daki ne mai cin dakuna sama da uku. Ya ga tarin dukiyar da ko a tunani bai taba zaton akwai irinta ba a fadin duniya. 
Komai bangarensa dabam,zinariya da azurfa da tagulla da tsabar kudi,ga su nan bila haddin. Ba tare da bata lokaci ba,
ya fara cika mangalolinsa da ita yana tunanin abubuwan da zai yi idan ya kwashe ta duka ya kai gida.

Da ya gama cika mangalolinsa,ya ga kamar ma bai debi komai ba,domin babu alamun dukiyar nan ta ragu. Ya kiyasta cewa koda zai kwashe dukiyan nan duka,
to sai ya yi wata uku ko fiye yana zuwa kullum yana dibar ta. Ya zo inda kofar dutsen ta ke ya ce, "Fayau, bude dutsen Cimcim." dutse ya ki budewa. 
Ya kara cewa, "Fayau,bude dutsen Jimjim." Dutse bai ko motsa ba.

Kasim yayi ta kiran kalmomi kamar su,Timtim, Kimkim, Zimzim, amma Allah da ikonsa har ya gaji ya kasa tuna kalmar "Simsim".
Kamar ma da dai bai taba jin kalmar ba.
Daga nan sai murna ta koma ciki,domin ya tabbata idan barayin nan suka dawo suka same shi a ciki,lalle kashinsa ya bushe.

Sai duk dukiyar da ke cikin dutsen ta fita daga ransa,ya fara safa da marwa yana kokarin tuna kalmar da ake fada dutsen ya bude. 
Yayi duk iyakar kokarinsa amma ya kasa tuna kalmar.
Da ya gaji sai ya sami wuri ya zauna yana tunanin makomarsa idan barayin nan suka same shi a cikin ma'ajiyarsu.

Bai san tsawon lokacin da ya kwashe a cikin dutsen ba. Can sai ya ji karar kofatan dawaki suna nufo wurin da dutsen ya ke. 
Tun yana jiyo su daga nesa, har suka zo daf da gindin dutsen. 
Daga nan sai ya ji duk sun sauka daga kan dawakansu. Ya duba cikin dutsen nan ko zai ga wani makami da zai kare kansa da shi,bai samu ba.
 Ya duba ko akwai wani wuri da zai iya boyewa,ya ga babu.
 Ya yanke shawarar ya tsaya daf da bakin kofa, idan dutsen ya bude sai ya yi wuf ya yi waje da gudu ya kama dokinsu daya ya sukwane shi, 
idan Allah ya taimake shi zai iya tserewa. Don haka sai ya tsaya daf da wurin da kofar za ta bude cikin shiri.

Su kuwa barayin nan da suka zo gindin dutse sai suka ga jakai guda goma a daure, suka duba ko'ina ba su ga mai su ba. Sai jikinsu ya ba su,
domin ba su taba sa ran wani dan Adam zai iya zuwa cikin wannan daji ba,kuma har gindin dutsensu.Babbansu ya matsa gaban dutsen ya ce,
"Fayau, bude dutsen Simsim." Nan take dutse ya bude.

*** *** ***

ZA MU CI GABA RANAR SATI MAI ZUWA,DAI DAI WANNAN LOKACI,INSHA ALLAH.
Waziri Aku #NISHAAADDI management.

Thursday 26 September 2013

01. HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN


Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan sarakuna. 
Shi ne mafi tsarki daga dukkan abubuwa. 
Tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa kuma Annabinsa,Muhammadu dan Amina (SAW).

A wani shudadden zamani,a wani gari na cikin kasar Farisa,an yi wadan su mazaje guda biyu yan uwan juna. 
Babban sunansa Kasim karamin kuwa sunansa Ali Baba. 
Bayan rasuwar mahaifinsu,aka raba musu gadon yar dukiyar da ya bari,kowa ya kwashi rabonsa.

Kasim ya auri yar wani babban attajiri na garin,shi kuwa Ali Baba ya auri wata yarinya wacce iyayenta sun kasance talakawa ne. 
Ba a dade ba,sai surukin Kasim ya mutu,yarsa ta gaji dukkan dukiyarsa,domin ita kadai ce yar da ke gare shi.
Ita kuma ta damka dukiyar nan a hannun mijinta Kasim. 
Nan take Kasim ya zama babban attajirin da babu kamar sa a duk fadin garin.

Shi kuwa Ali Baba sai ya kasance dan abin da ya gada na dukiya daga mahaifinsu ya kare.
Ya zama talaka wanda bai mallaki komai ba sai jakai guda uku. 
Sai ya rika zuwa daji da jakansa yana saran itace yana lafto wa jakan nan yana kawowa cikin gari.
Idan ya sayar,ya siyo abincin da za su ci,shi da matarsa.

Ana nan haka kullum,wata rana Ali Baba ya shiga daji domin yin sana'arsa kamar yadda ya saba. 
Bayan ya gama dora wa jakansa itace,yana haramar ya kora su ya tafi,sai ya hango 'kura ta toshe sararin samaniya daga nesa,
ta tinkaro inda ya ke. Ya ga cewa idan ya ci gaba da tafiya mahayan nan za su cim masa,sai ya kora jakansa cikin rami, 
shi kuwa ya sami wata babbar itaciya mai duhuwa,wacce zai iya ganin abin da ya ke kasa ba tare da wanda ke kasa ya gan shi ba,ya haye.

Bai jima da hawa saman itaciyar nan ba,sai ya hango mutane akan dawaki a sukwane sun nufo inda ya ke. 
Suna zuwa wurin,sai duk suka ja suka tsaya. Kowane daga cikinsu ya sauka daga kan dokinsa,ya daure shi. 
Ali Baba ya dube su da kyau, ya ga cewa dukkansu samari ne majiya karfi,kowane yana rataye da takobi, 
yana dauke da kaya a kan dokinsa.Ya kirga su,ya ga cewa su arba'in ne cif.

Ashe mutanen nan barayi ne,masu tare fatake suna yi musu fashi,yanzu ma sun zo ne wurin da suke boye kayan da suke satowa. 
Ali Baba ya ga daya daga cikinsu,wanda yana zaton shi ne babbansu,ya tafi gindin wani dutse da ciyawa ta lullube shi,
wanda idan ba yanzu ba Ali Baba bai taba lura da akwai dutse wurin ba. Ya tsaya gaban dutsen ya ce,
"Fayau,bude dutsen Simsim." Dutse ya tsaga gida biyu, sai ga kofa ta bayyana. 
Barayin nan suka yi ta duruwa ciki da kayan da suka sato,bayan kowa ya shige,sai babban ya bi daga baya. 
Yana shigewa,sai dutsen ya koma ya rufe,tamkar babu dutse a wurin.

Ali Baba yana kan bishiya, yana kallon dukkan abin da ke faruwa.Bayan barayin nan sun shige cikin dutse,sai yayi kamar ya sauko ya kama doki daya ya hau, 
ya kora jakansa ya tsere,sai kuma ya tuna idan ya sauko kuma aka yi rashin sa'a da barayin nan suna fitowa daga dutsen nan,lalle za su kama shi.
Saboda haka sai ya canza shawara,ya ci gaba da zama a kan bishiyar.

Can zuwa wani lokaci sai ya ga kofar dutsen nan ta bude,shugaban barayin ya fara fitowa ya tsaya a gaban kofar yana kidaya barayin nan a lokacin da suke fitowa, 
har ya kidaya talatin da tara, gami da shi arba'in ke nan.Da suka gama fitowa,sai Ali Baba ya ji ya ce,"Garam, rufe dutsen Simsim." dutse ya koma ya rufe. 
Suka hau dawakinsu suka juya ta hanyar da suka fito.

Da Ali Baba ya ga kurarsu ta bace,ya sauko daga kan itaciya,ya nufi inda ya boye jakansa da sauri domin ya kora su zuwa gida, 
sai wata zuciya ta ce masa,"Ka gwada fadin kalmomin nan ka ga ko dutsen nan zai bude.
" Ya tafi gaban dutsen ya tsaya dai dai inda ya ga shugaban barayin nan ya tsaya, ya ce,"Fayau, bude dutsen Simsim." Yana fadar haka kuwa sai kofa ta bude.

Ali Baba ya kutsa kai cikin dutsen nan.Yana shiga sai dutse ya koma ya rufe.Da farko yayi zaton zai ga duhu dindim a ciki,amma sai ya ga haske kamar an kunna fitilu. 
Ya duba haka,sai ya ga dukiya tsibi-tsibi.Tsibin zinariya daban,tsibin azurfa daban,na tagulla daban,gefe kuma ga kudi nan tsaba cunkus. 
Ali Baba yayi mamakin yadda wadan nan barayi suka tara dukiya mai yawa haka.Ya ce a ransa,lalle sun gaji dutsen nan ne tun daga kaka da kakanni,
domin yawan su ba su isa su tara wannan dukiya ba koda kuwa sun yi shekara dari suna tara ta.

Ya tattaro wasu buhuhuwan zinariya, wadan da ya san jakansa za su iya dauka. Ya ce "Fayau, bude dutsen Simsim." Dutse ya bude ya fito da buhuhuwan waje,sannan ya ce, 
"Garam rufe dutsen Simsim." Dutse ya koma ya rufe.Ya jawo jakansa ya dora musu dukiyar nan sannan ya dora musu itace daga sama ya rufe yadda mutane ba za su gane ba.
 Ya kora jakunan sa da sauri ya nufi gida yana murna.

Da ya isa gida,ya kora jakunan ciki ya kira matarasa suka sauke kayan.Koda ya zazzage,sai wurin ya haske,matar ta ga zinariya tana daukar ido. 
Ya shaida mata dukkan abin da ya faru.Ta yi godiya ga Allah ta ce, "Dare daya Allah kan yi bature,
hakika duk fadin garin nan yanzu babu wanda ya kai mu arziki. Bari na kidaya na gani" 

Ali Baba ya yi dariya ya ce "Mene ne na batan lokacinki wajen kidaya wannan zinariya? Sai ki yi kwanki ba ki gama gidaya ta ba. 
Abin da na ke so da ke shi ne,bakinki kanen kafarki,kada ki kuskura wani ya ji wannan labari. Zan je na haka rami mu binne wannan dukiya da Allah ya ba mu."

Matar ta ce,"Duk da haka dai ina so na san adadin wannan zinariya.Kafin ka gama haka rami bari na je nan makwabtanmu, 
gidan yayanka Kasim na aro karamin mudunsu na awon hatsi domin na ga ko mudu nawa wannan zinariya za ta yi."

Ya ce ba laifi amma ta tabbatar ba ta fadawa kowa abin da za ta auna da mudun ba.Ta fito ta shiga gidan Kasim,ta taras da matarsa. 
Bayan sun gaisa ta ce ta zo ne aron mudunsu na awon hatsi.Matar Kasim ta tambaye ta babba ko karami? Ta ce karamin ma zai yi.
Ta shiga cikin daki domin ta dauko ma ta,ta ce a ranta me wadan nan matsiyatan za su yi da mudu? Ina kuma suka sami hatsi mai yawa haka da har sai sun auna shi da mudu?
Kuma wane irin hatsi ne wannan? Sai ta sami karo kadan ta manna shi a cikin kusurwar mudun wanda ta tabbata karon zai like kwaya daya ta hatsin da za a auna, 
ta haka za ta iya gano kalar hatsin da suka auna idan an maido mata da mudun.Ta kawo wa matar Ali Baba.

Bayan ta dawo gida, sai ta fara auna zinariyar nan mudu-mudu har ta gama kaf.Ta je ta sahida wa mijinta da yake hakar rami ko mudu nawa ta auna.Ta ce za ta je ta mayar musu da mudunsu. 
Ashe ba ta lura ba,kwayar zinariya daya ta manne da karon nan a can kasan mudun. Da matar Kasim ta karbi mudu, bayan matar Ali Baba ta tafi,sai ta duba cikin mudun. 
Wani irin mamaki ya rufe ta lokacin da ta ga kwayar zinariya a cikin mudun.

Nan take hassada ta daki kirjinta ta ce ashe Ali Baba har yana da zinariyar da ta fi karfin a kidaya ta da hannu sai dai awo da mudu.Ina ya sami wannan dukiya? Ko ya fara sata ne?
Bari mijina ya dawo in fada masa halin da kanensa yake ciki.

*** *** ***
ZA MU CI GABA GOBE INSHA'A RABBA.
*******JUMA'A TA GARI #NISHAAADDI
                                                                                                        
                                                                                                                                      Waziri Aku.

Wednesday 18 September 2013

LOVE = KAUNA


                        ---Haruffa hudu masu furanni 
                              zanyo wasa da tsagun ko wannansu

Harafin farko inibin raina,
sukari a shafin kirjina,
kwance yake kuma,
gashi tsaye akan kansa.


Harafi na biyu idon basirata,
gwanda koshi babu,
abarba gidan zaƙi.


Harafi na uku lafazin rayuwata,
malam buɗe mana littafi,
tarbo mani harafinnan na karshe.


Wato harafinnan na huɗu,
kafin na rikece nabi duniya,
neman harafinnan  na daban,
me hakora hawa gida uku.

*Ina mai mika godiyata ga lecturer ismail bala bayero unversity,kano.
Wanda jin ko nace samun amincewarsa ayau na yimin editin littafina wanda na kammala rubu tawa wato "KAUNAR ZAMANI",ya hanani bacci har na kirkiri wannan poem din dake sama a daidai karfe daya da minti arba'in da uku(1:43am).

Jama'armu na #Nishaaaddi ni ne dai naku IBrahim BaBa,tsokar runbum Nishaaaddi,ina mai muku alkawarin tsokaci daga littafin nawa ranar jumma'a,duk da dai nasan yana iya sauya salo bayan angama editin dinsa.
(ALLAH ya gwada mana ranar launcinsa/launch).


Saturday 14 September 2013

KACICI KACICI

1-  Salamun gaisuwa tagari,
2-  Ga Manzo na abin fahari,
3-  Sahabbai masu yin witiri,
4-  Da alaye da ke da gari!
5-  Tabaraka mai dukkan lamari,
6-  Ka ɗauke min duhun kabari,
7-  Gare ka na ke daɗin zikiri,
8-  Ka ban ’yar nan abar garari!
9-  A yau dai na fito sarari,

10-  A yaƙin ban ganin haɗari,
11-  Kamar yaro a ba shi ɗari:
12-  A murna ya fi mai digiri!
13-  Abokai na ku yo nazari:
14-  Ga rana ta fito sarari,
15-  Ta na haske, ta na ta fari,
16-  Hasken rai na abar marari!
17-  Budurwa ce fara tagari,
18-  Mai murya sai ka ce kanari,
19-  A baitoci da ke waɗari,
20- A ƙauye ko cikin sa gari!
21-  Da ke ce yau na ke fahari,
22-  A zuci a yau ina tiriri,
23-  Soyayya ta saka ni jiri,
24-  Batun ƙaunar ki ba ni bari!
25-  Mai so na sai mu ƙara shiri,
26-  Mu sha zaƙi na so nagari,
27-  Shi zaƙin sai ka ce sikari,
28-  Tsaya kai na ki na jimiri!
29-  Abar ƙauna abar garari,
30-  Kin taka rawa kamar mazari,
31-  Me zan ce ne ki ba ni gari,
32-  Har in dace da ke tagari?
33-  Mafarki na abar marari,
34-  In rintse ido kamar kanari,
35-  In farka ga ki nan sarari
36-  A tare da ni mu na bidiri!
37-  In buɗe ido cikin katari,
38-  A ce ni ne na cinye gari,
39-  A ɗaki na ki ke witiri,
40-  A lallai da’iman lamari!
41-  Kira na sai mu ƙara shiri,
42-  Ga Allah mui ta yin witiri,
43-  Nabiyyul Lahu nai zikiri,

44-  Ku ce amin da ayyiriri!


-----------Godiya ta musamman ga: Ibrahim shema Da Bashir muhammad idris