Saturday 28 September 2013

02 HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN


Lokacin da Kasim ya dawo daga kasuwa tun bai huta ba,matarsa ta tare shi ta ce,
"Maigida,na san da cewa ka dauki kanka a matsayin wanda ya fi kowa arziki a duk fadin garin nan,
to amma abin da ba ka sani ba shi ne,yanzu akwai wanda ya dame ka ya shanye game da arziki cikin wannan gari namu. 
Domin yana da tarin zinariyar da ta fi karfin a kidaya ta da hannu sai dai a auna ta da mudu."

Kasim ya ce,"Wane ne wannan attajiri haka,amma dai bai dade da zuwa garin nan ba ko?"
Matar ta ce,"Ba kowa ba ne face dan uwanka Ali Baba." Ta kwashe dukkan labarin yadda matar Ali Baba ta zo aron mudu a wurinta,
da kuma dabarar da ta yi har ta gano abin da aka auna da mudun. 

Kasim ya kasance ba ya kula da taimakon dan uwansa Ali Baba duk da tarin dukiyarsa,
ba ya ko yarda ya matso kusa gare shi,wai kada ya shafa masa talauci.
Da ya ji wannan labari daga matarsa,sai ya cika da mamaki tare kuma da hassadar jin cewa wai har akwai wanda ya fi shi arziki a garinsu. 
Ya ce a cikin ransa,"Yanzu dare ya yi,amma gobe tunda safe zan je gidan dan uwana na ji inda ya sami wannan dukiya da rana tsaka.Lalle idan ya fara sata ne,
zan tsegunta wa Sarki a daure shi." Ya kwanta amma ya kasa yin barci,yana ta kahon dandi har gari ya waye.

Da gari ya waye,tunda sassafe Kasim ya sallama wa Ali Baba.Bayan ya fito,ko gaisawa ba su yi ba,sai Kasim ya ce,"Ali Baba ka yi wa mutane badda sau,
suna ganin ka a matsayin talaka wanda bai mallaki komai ba sai jakai guda uku da kake zuwa daji kana yiwo itacen siyarwa.
Amma abin mamaki, jiya bayan na dawo daga shagona,matata ta ba ni wannan kwayar zinariyar ta ce mini a cikin mudun da ta ara muku ta makale.
Wannan ya tabbatar mata da cewa ba hatsi kuka auna da mudun ba.
Wannan ne dalilin da ya sa yanzu na yo maka sammako domin na ji inda ka sami wannan dukiya, 
idan kuwa ka ki fada mini zan je na shaida wa Sarki cewa kana daya daga cikin barayin nan da suka addabi mutanen wannan gari da kewayensa da sata,
yanzu haka ma zinariya na nan kime a gidanka da kuka sato. Kuma na tabbata idan aka bincike gidanka kaf,za a gan ta."

Da Ali Baba ya ji wannan zance na dan uwansa,sai ya tabbatar da cewa matarsa ta fallasa musu sirrinsu ba tare da ta sani ba,
don haka babu wani boye-boye illa ya fada wa dan uwansa gaskiyar abin da ya faru.

Ali Baba ya kwashe labrin abinda ya faru duka ya fada wa Kasim.
Ya yi masa kwatancen dajin nan da kuma dai dai wurin da dutsen da barayin nan suke tara dukiyarsu ya ke. 
Ya kuma fada masa abin da ake cewa dutsen ya bude da kuma abin da ake cewa ya rufe.

Kasim na gama jin wannan labari,bai zame ko'ina ba sai kasuwa.Ya siyo jakai guda goma,kowane da mangalarsa,ya kawo gida ya daure.
Tun da asuba ya daura wa jakuna mangaloli, ya nufi dajin nan da Ali Baba ya yi masa kwatance. Can zuwa rana tsaka ya isa,
ya bi kwatancen da aka yi masa har ya gano wurin da dutsen ya ke. Ya daure dabbobinsa a kusa da dutsen.

Ya tsaya gindin dutse ya ce,"Fayau, bude dutsen Simsim." Rufe bakinsa ke da wuya, sai ya ga kofa ta bude daga jikin dutsen. Mamaki ya rufe shi, 
nan da nan ya kwanto mangaloli daga jakunansa ya kutsa kai cikin dutsen, yana shiga dutsen ya rufe.

Kasim ya ga ashe dutsen wani katon daki ne mai cin dakuna sama da uku. Ya ga tarin dukiyar da ko a tunani bai taba zaton akwai irinta ba a fadin duniya. 
Komai bangarensa dabam,zinariya da azurfa da tagulla da tsabar kudi,ga su nan bila haddin. Ba tare da bata lokaci ba,
ya fara cika mangalolinsa da ita yana tunanin abubuwan da zai yi idan ya kwashe ta duka ya kai gida.

Da ya gama cika mangalolinsa,ya ga kamar ma bai debi komai ba,domin babu alamun dukiyar nan ta ragu. Ya kiyasta cewa koda zai kwashe dukiyan nan duka,
to sai ya yi wata uku ko fiye yana zuwa kullum yana dibar ta. Ya zo inda kofar dutsen ta ke ya ce, "Fayau, bude dutsen Cimcim." dutse ya ki budewa. 
Ya kara cewa, "Fayau,bude dutsen Jimjim." Dutse bai ko motsa ba.

Kasim yayi ta kiran kalmomi kamar su,Timtim, Kimkim, Zimzim, amma Allah da ikonsa har ya gaji ya kasa tuna kalmar "Simsim".
Kamar ma da dai bai taba jin kalmar ba.
Daga nan sai murna ta koma ciki,domin ya tabbata idan barayin nan suka dawo suka same shi a ciki,lalle kashinsa ya bushe.

Sai duk dukiyar da ke cikin dutsen ta fita daga ransa,ya fara safa da marwa yana kokarin tuna kalmar da ake fada dutsen ya bude. 
Yayi duk iyakar kokarinsa amma ya kasa tuna kalmar.
Da ya gaji sai ya sami wuri ya zauna yana tunanin makomarsa idan barayin nan suka same shi a cikin ma'ajiyarsu.

Bai san tsawon lokacin da ya kwashe a cikin dutsen ba. Can sai ya ji karar kofatan dawaki suna nufo wurin da dutsen ya ke. 
Tun yana jiyo su daga nesa, har suka zo daf da gindin dutsen. 
Daga nan sai ya ji duk sun sauka daga kan dawakansu. Ya duba cikin dutsen nan ko zai ga wani makami da zai kare kansa da shi,bai samu ba.
 Ya duba ko akwai wani wuri da zai iya boyewa,ya ga babu.
 Ya yanke shawarar ya tsaya daf da bakin kofa, idan dutsen ya bude sai ya yi wuf ya yi waje da gudu ya kama dokinsu daya ya sukwane shi, 
idan Allah ya taimake shi zai iya tserewa. Don haka sai ya tsaya daf da wurin da kofar za ta bude cikin shiri.

Su kuwa barayin nan da suka zo gindin dutse sai suka ga jakai guda goma a daure, suka duba ko'ina ba su ga mai su ba. Sai jikinsu ya ba su,
domin ba su taba sa ran wani dan Adam zai iya zuwa cikin wannan daji ba,kuma har gindin dutsensu.Babbansu ya matsa gaban dutsen ya ce,
"Fayau, bude dutsen Simsim." Nan take dutse ya bude.

*** *** ***

ZA MU CI GABA RANAR SATI MAI ZUWA,DAI DAI WANNAN LOKACI,INSHA ALLAH.
Waziri Aku #NISHAAADDI management.

Thursday 26 September 2013

01. HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN


Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan sarakuna. 
Shi ne mafi tsarki daga dukkan abubuwa. 
Tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa kuma Annabinsa,Muhammadu dan Amina (SAW).

A wani shudadden zamani,a wani gari na cikin kasar Farisa,an yi wadan su mazaje guda biyu yan uwan juna. 
Babban sunansa Kasim karamin kuwa sunansa Ali Baba. 
Bayan rasuwar mahaifinsu,aka raba musu gadon yar dukiyar da ya bari,kowa ya kwashi rabonsa.

Kasim ya auri yar wani babban attajiri na garin,shi kuwa Ali Baba ya auri wata yarinya wacce iyayenta sun kasance talakawa ne. 
Ba a dade ba,sai surukin Kasim ya mutu,yarsa ta gaji dukkan dukiyarsa,domin ita kadai ce yar da ke gare shi.
Ita kuma ta damka dukiyar nan a hannun mijinta Kasim. 
Nan take Kasim ya zama babban attajirin da babu kamar sa a duk fadin garin.

Shi kuwa Ali Baba sai ya kasance dan abin da ya gada na dukiya daga mahaifinsu ya kare.
Ya zama talaka wanda bai mallaki komai ba sai jakai guda uku. 
Sai ya rika zuwa daji da jakansa yana saran itace yana lafto wa jakan nan yana kawowa cikin gari.
Idan ya sayar,ya siyo abincin da za su ci,shi da matarsa.

Ana nan haka kullum,wata rana Ali Baba ya shiga daji domin yin sana'arsa kamar yadda ya saba. 
Bayan ya gama dora wa jakansa itace,yana haramar ya kora su ya tafi,sai ya hango 'kura ta toshe sararin samaniya daga nesa,
ta tinkaro inda ya ke. Ya ga cewa idan ya ci gaba da tafiya mahayan nan za su cim masa,sai ya kora jakansa cikin rami, 
shi kuwa ya sami wata babbar itaciya mai duhuwa,wacce zai iya ganin abin da ya ke kasa ba tare da wanda ke kasa ya gan shi ba,ya haye.

Bai jima da hawa saman itaciyar nan ba,sai ya hango mutane akan dawaki a sukwane sun nufo inda ya ke. 
Suna zuwa wurin,sai duk suka ja suka tsaya. Kowane daga cikinsu ya sauka daga kan dokinsa,ya daure shi. 
Ali Baba ya dube su da kyau, ya ga cewa dukkansu samari ne majiya karfi,kowane yana rataye da takobi, 
yana dauke da kaya a kan dokinsa.Ya kirga su,ya ga cewa su arba'in ne cif.

Ashe mutanen nan barayi ne,masu tare fatake suna yi musu fashi,yanzu ma sun zo ne wurin da suke boye kayan da suke satowa. 
Ali Baba ya ga daya daga cikinsu,wanda yana zaton shi ne babbansu,ya tafi gindin wani dutse da ciyawa ta lullube shi,
wanda idan ba yanzu ba Ali Baba bai taba lura da akwai dutse wurin ba. Ya tsaya gaban dutsen ya ce,
"Fayau,bude dutsen Simsim." Dutse ya tsaga gida biyu, sai ga kofa ta bayyana. 
Barayin nan suka yi ta duruwa ciki da kayan da suka sato,bayan kowa ya shige,sai babban ya bi daga baya. 
Yana shigewa,sai dutsen ya koma ya rufe,tamkar babu dutse a wurin.

Ali Baba yana kan bishiya, yana kallon dukkan abin da ke faruwa.Bayan barayin nan sun shige cikin dutse,sai yayi kamar ya sauko ya kama doki daya ya hau, 
ya kora jakansa ya tsere,sai kuma ya tuna idan ya sauko kuma aka yi rashin sa'a da barayin nan suna fitowa daga dutsen nan,lalle za su kama shi.
Saboda haka sai ya canza shawara,ya ci gaba da zama a kan bishiyar.

Can zuwa wani lokaci sai ya ga kofar dutsen nan ta bude,shugaban barayin ya fara fitowa ya tsaya a gaban kofar yana kidaya barayin nan a lokacin da suke fitowa, 
har ya kidaya talatin da tara, gami da shi arba'in ke nan.Da suka gama fitowa,sai Ali Baba ya ji ya ce,"Garam, rufe dutsen Simsim." dutse ya koma ya rufe. 
Suka hau dawakinsu suka juya ta hanyar da suka fito.

Da Ali Baba ya ga kurarsu ta bace,ya sauko daga kan itaciya,ya nufi inda ya boye jakansa da sauri domin ya kora su zuwa gida, 
sai wata zuciya ta ce masa,"Ka gwada fadin kalmomin nan ka ga ko dutsen nan zai bude.
" Ya tafi gaban dutsen ya tsaya dai dai inda ya ga shugaban barayin nan ya tsaya, ya ce,"Fayau, bude dutsen Simsim." Yana fadar haka kuwa sai kofa ta bude.

Ali Baba ya kutsa kai cikin dutsen nan.Yana shiga sai dutse ya koma ya rufe.Da farko yayi zaton zai ga duhu dindim a ciki,amma sai ya ga haske kamar an kunna fitilu. 
Ya duba haka,sai ya ga dukiya tsibi-tsibi.Tsibin zinariya daban,tsibin azurfa daban,na tagulla daban,gefe kuma ga kudi nan tsaba cunkus. 
Ali Baba yayi mamakin yadda wadan nan barayi suka tara dukiya mai yawa haka.Ya ce a ransa,lalle sun gaji dutsen nan ne tun daga kaka da kakanni,
domin yawan su ba su isa su tara wannan dukiya ba koda kuwa sun yi shekara dari suna tara ta.

Ya tattaro wasu buhuhuwan zinariya, wadan da ya san jakansa za su iya dauka. Ya ce "Fayau, bude dutsen Simsim." Dutse ya bude ya fito da buhuhuwan waje,sannan ya ce, 
"Garam rufe dutsen Simsim." Dutse ya koma ya rufe.Ya jawo jakansa ya dora musu dukiyar nan sannan ya dora musu itace daga sama ya rufe yadda mutane ba za su gane ba.
 Ya kora jakunan sa da sauri ya nufi gida yana murna.

Da ya isa gida,ya kora jakunan ciki ya kira matarasa suka sauke kayan.Koda ya zazzage,sai wurin ya haske,matar ta ga zinariya tana daukar ido. 
Ya shaida mata dukkan abin da ya faru.Ta yi godiya ga Allah ta ce, "Dare daya Allah kan yi bature,
hakika duk fadin garin nan yanzu babu wanda ya kai mu arziki. Bari na kidaya na gani" 

Ali Baba ya yi dariya ya ce "Mene ne na batan lokacinki wajen kidaya wannan zinariya? Sai ki yi kwanki ba ki gama gidaya ta ba. 
Abin da na ke so da ke shi ne,bakinki kanen kafarki,kada ki kuskura wani ya ji wannan labari. Zan je na haka rami mu binne wannan dukiya da Allah ya ba mu."

Matar ta ce,"Duk da haka dai ina so na san adadin wannan zinariya.Kafin ka gama haka rami bari na je nan makwabtanmu, 
gidan yayanka Kasim na aro karamin mudunsu na awon hatsi domin na ga ko mudu nawa wannan zinariya za ta yi."

Ya ce ba laifi amma ta tabbatar ba ta fadawa kowa abin da za ta auna da mudun ba.Ta fito ta shiga gidan Kasim,ta taras da matarsa. 
Bayan sun gaisa ta ce ta zo ne aron mudunsu na awon hatsi.Matar Kasim ta tambaye ta babba ko karami? Ta ce karamin ma zai yi.
Ta shiga cikin daki domin ta dauko ma ta,ta ce a ranta me wadan nan matsiyatan za su yi da mudu? Ina kuma suka sami hatsi mai yawa haka da har sai sun auna shi da mudu?
Kuma wane irin hatsi ne wannan? Sai ta sami karo kadan ta manna shi a cikin kusurwar mudun wanda ta tabbata karon zai like kwaya daya ta hatsin da za a auna, 
ta haka za ta iya gano kalar hatsin da suka auna idan an maido mata da mudun.Ta kawo wa matar Ali Baba.

Bayan ta dawo gida, sai ta fara auna zinariyar nan mudu-mudu har ta gama kaf.Ta je ta sahida wa mijinta da yake hakar rami ko mudu nawa ta auna.Ta ce za ta je ta mayar musu da mudunsu. 
Ashe ba ta lura ba,kwayar zinariya daya ta manne da karon nan a can kasan mudun. Da matar Kasim ta karbi mudu, bayan matar Ali Baba ta tafi,sai ta duba cikin mudun. 
Wani irin mamaki ya rufe ta lokacin da ta ga kwayar zinariya a cikin mudun.

Nan take hassada ta daki kirjinta ta ce ashe Ali Baba har yana da zinariyar da ta fi karfin a kidaya ta da hannu sai dai awo da mudu.Ina ya sami wannan dukiya? Ko ya fara sata ne?
Bari mijina ya dawo in fada masa halin da kanensa yake ciki.

*** *** ***
ZA MU CI GABA GOBE INSHA'A RABBA.
*******JUMA'A TA GARI #NISHAAADDI
                                                                                                        
                                                                                                                                      Waziri Aku.

Wednesday 18 September 2013

LOVE = KAUNA


                        ---Haruffa hudu masu furanni 
                              zanyo wasa da tsagun ko wannansu

Harafin farko inibin raina,
sukari a shafin kirjina,
kwance yake kuma,
gashi tsaye akan kansa.


Harafi na biyu idon basirata,
gwanda koshi babu,
abarba gidan zaƙi.


Harafi na uku lafazin rayuwata,
malam buɗe mana littafi,
tarbo mani harafinnan na karshe.


Wato harafinnan na huɗu,
kafin na rikece nabi duniya,
neman harafinnan  na daban,
me hakora hawa gida uku.

*Ina mai mika godiyata ga lecturer ismail bala bayero unversity,kano.
Wanda jin ko nace samun amincewarsa ayau na yimin editin littafina wanda na kammala rubu tawa wato "KAUNAR ZAMANI",ya hanani bacci har na kirkiri wannan poem din dake sama a daidai karfe daya da minti arba'in da uku(1:43am).

Jama'armu na #Nishaaaddi ni ne dai naku IBrahim BaBa,tsokar runbum Nishaaaddi,ina mai muku alkawarin tsokaci daga littafin nawa ranar jumma'a,duk da dai nasan yana iya sauya salo bayan angama editin dinsa.
(ALLAH ya gwada mana ranar launcinsa/launch).


Saturday 14 September 2013

KACICI KACICI

1-  Salamun gaisuwa tagari,
2-  Ga Manzo na abin fahari,
3-  Sahabbai masu yin witiri,
4-  Da alaye da ke da gari!
5-  Tabaraka mai dukkan lamari,
6-  Ka ɗauke min duhun kabari,
7-  Gare ka na ke daɗin zikiri,
8-  Ka ban ’yar nan abar garari!
9-  A yau dai na fito sarari,

10-  A yaƙin ban ganin haɗari,
11-  Kamar yaro a ba shi ɗari:
12-  A murna ya fi mai digiri!
13-  Abokai na ku yo nazari:
14-  Ga rana ta fito sarari,
15-  Ta na haske, ta na ta fari,
16-  Hasken rai na abar marari!
17-  Budurwa ce fara tagari,
18-  Mai murya sai ka ce kanari,
19-  A baitoci da ke waɗari,
20- A ƙauye ko cikin sa gari!
21-  Da ke ce yau na ke fahari,
22-  A zuci a yau ina tiriri,
23-  Soyayya ta saka ni jiri,
24-  Batun ƙaunar ki ba ni bari!
25-  Mai so na sai mu ƙara shiri,
26-  Mu sha zaƙi na so nagari,
27-  Shi zaƙin sai ka ce sikari,
28-  Tsaya kai na ki na jimiri!
29-  Abar ƙauna abar garari,
30-  Kin taka rawa kamar mazari,
31-  Me zan ce ne ki ba ni gari,
32-  Har in dace da ke tagari?
33-  Mafarki na abar marari,
34-  In rintse ido kamar kanari,
35-  In farka ga ki nan sarari
36-  A tare da ni mu na bidiri!
37-  In buɗe ido cikin katari,
38-  A ce ni ne na cinye gari,
39-  A ɗaki na ki ke witiri,
40-  A lallai da’iman lamari!
41-  Kira na sai mu ƙara shiri,
42-  Ga Allah mui ta yin witiri,
43-  Nabiyyul Lahu nai zikiri,

44-  Ku ce amin da ayyiriri!


-----------Godiya ta musamman ga: Ibrahim shema Da Bashir muhammad idris

Tuesday 10 September 2013

Duniyar Karya


A shekara ta dubu biyu da takwas (2008) a bisa dandalin sadarwa da ake kira 'facebook' ina ta rubuta tsokaci da kuma tura hotuna,inata nishadi na 

Kwatsam sai na hadu da ita,tayi ikirarin nine soyayyar rayuwar ta,ta cika ni da sakon ni 'e-mail', kuma na ji dadin duk wannan tarairaya,bisa ga dukkan alamu tana cikin kadaici kuma tana neman ta shiga soyayya. 

Ya kasance ranar alhamis sai na canza adireshin e-mail dina zuwa ga lambar waya na saboda e-mail din nawa na bani matsala,don haka yasa na barshi kafin na samu kyaransa
Ina dawowa gida bayan na sha gwagwarmaya a makaranta, sai wayar selula ta tai kara,murya mai dadi ta biyo bayan hakan ta gabatar da kanta a matsayin Firdausi Mahmud.

Ta sanar dani cewa wani kundin soyayya ne take nufi na dashi,har ta kaiga tattaro zuciya ta,ta ce tana kauna ta,a wannan halin na sha dariyata
Saboda ko kadan ban dauka da gaske take yi ba, na zaci raha ta kawo domin ta sani nishadi, amma sai ta karyata ni a bisa hakan.
Kosawa ta kama ni, har na kaiga duba shafin ta da kuma hotunan ta, abun da idanuwa na suka gani ya birge zuciyata, tunda tana cikin bukatan aboki ni kuma a shirye nike da shiga sabon lamari, kuma babu abin haufi a gareni sai muka fara ganawa akai-akai.
Ta yi ta nanata irin soyayyar da take min, cikin 'yan kwanaki kadan muka fara magana tamkar soyayyar mu ta dauko asali ne tun yarunta, har sai da ta sauya tunani na zuwa ga zaton qila mu zamto ma'auratan juna.
Na tuna kalmomin ta, ta taba gaya min cewar nine abin da tafi so kuma ba zata taba ajiye ni ba domin daukan wani abu komin dadin sa.
Mun shirya haduwa saboda tana zaune ne a abuja yayin da ni kuma a Lagos nike, da na sauka sai dan'uwan ta ya shigar dani cikin gidan su, suna da azirki sosai idanuwa na sun gaskata min da haka.
Amma a yayin da na kyalla idona akan sarauniyar tawa, sai na dimautu/dimauce, kuma gashi tausayi ba zai bari nai mata rashin adalci ba, amma kuma ta boye min wani abu da sai ayau na gane wa kaina.
Tabbas itace yarinyar da na gani a hoto, cike da kyawo amma sai dai kafa daya kawai gare ta.

****Zayyana min abin da za kayi/ ko zaki yi, idan hakan ta kasance gareka/ki a matsayin da na samu kai na aciki****
Ku ziyarci mu a: facebook.com/nishaaaddi
Twitter:@Ni_shaaaddi
Email:nishaaadi@gmail.com

Yar baba

Wayyo Allah na,itace taura-ran dake haska birnin
zuciyata,ta mallaki zuciyata tamkar itace ta halicceta
Abirnin zuciyata itace farin wata sha kallo

Ya gimbiyata.sanki na dasa wa zuciyata dadi kuma
tuna ninki na sanya wa idanuwana rashin barci,

Ahalin yanxu ana zabga ruwa a unguwarmu,jaruminki
naso ya danyi rufe idanuwansa

Yaki saliha zoki rarrashi zuciyata ta barni na huta.